Ƙungiyar Take It Back Movement ta sanar da shirinta na gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na Najeriya a ranar 5 ga Agusta, 2026, domin nuna adawa da abin da ta bayyana a matsayin matsalolin da ke ci gaba da addabar ƙasar.
A cewar ƙungiyar, zanga-zangar za ta mayar da hankali ne kan matsalar rashin tsaro, tsadar rayuwa da kuma abin da ta ce na tabarbarewar tsarin dimokuraɗiyya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa masu shirya zanga-zangar sun ce manufarsu ita ce isar da saƙon damuwar ‘yan ƙasa cikin lumana, tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan da za su magance matsalolin da al’umma ke fuskanta.
Sai dai har zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da wannan sabon shirin zanga-zangar ba.