Ya gargadi gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu kan ta daina fada da damar fadin albarkacin baki da matsa wa ‘yan adawa.
Lauyan ya yi kira ga hukumar zabe ta kasa INEC ta bude kofa domin jam’iyyun da ke da akidar siyasa su samu damar rajista
Lauyan ya yi wannan bayanin ne lokacin da kasashen Yammacin Afrika ke sake fuskantar kalubalen juyin mulki.
Falana ya bayyana matsayarsa ne a shirin Politics Today na Channels Television, inda ya jaddada cewa matsalolin tattalin arziki, talauci, jahilci da rashin tsaro suna daga cikin manyan abubuwan da ke sa jama’a tawaye.
Ya ce idan ana son ingantacciyar dimokuradiyya, dole gwamnati ta bude sarari ga ’yancin fadin albarkacin baki, ta kare ’yancin dan kasa, kuma ta daina daukar suka a matsayin laifi.