Gwamnatin Najeriya da Masarautar Saudiyya sun rattaba hannu a kan sabuwar yarjejeniya (MoU) domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da soja tsakanin ƙasashen biyu.
A cewar wata sanarwa daga Ahmed Dan Wudil, Mataimaki na Musamman kan Yada Labarai ga Ministan Ƙasa na Tsaro, yarjejeniyar za ta haɗa da aiki tare a fannin tsaro, horon soja, musayar bayanan sirri, ƙera kayan tsaro da kuma ayyukan haɗin gwiwa domin tallafa wa dorewar tsaro.
Karamin Ministan Tsaro, Dr. Mohammed Bello Matawalle, ne ya sa wa yarjejeniyar hannu a madadin Najeriya, yayin da Dr. Khaleed H. Al-Biyari ya sa hannu a madadin Gwamnatin Masarautar Saudiyya.
Najeriya da Saudiyya za su karfafa alaka
Sanarwar ta bayyana cewa yarjejeniyar wani muhimmin mataki ne wajen zurfafa dangantaka da ƙarfafa ƙoƙarin hadin gwiwa domin fuskantar sabbin kalubalen tsaro.
Ta ce wannan haɗin gwiwa zai samar da ƙarin damar horo tare, ingantacciyar hanyar musayan bayanai da kuma aikin haɗin gwiwa a kan barazanar da duka ƙasashen ke fuskanta.
Jami’an ƙasashen biyu sun bayyana aniyarsu ta ganin wannan haɗin gwiwa ya amfanar kuma ya ƙara ƙarfin tsaron ƙasashensu.
Ma’aikatar Tsaro ta tarayya ta yi maraba da cigaban, tana mai cewa tana da kyakkyawan fata cewa matsalolin tsaro a wasu sassan Najeriya za su ragu sosai nan gaba kaɗan.
Ta jaddada cewa wannan sabuwar yarjejeniya za ta taimaka wajen ƙarfafa ikon Najeriya na yakar matsalolin tsaro yadda ya kamata.
Ma’aikatar ta ce yarjejeniyar ta nuna cewa Najeriya na da niyyar yin aiki tare da abokan hulɗa na duniya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.