Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS, Sanata Jibrin Barau, ya yaba wa gaggawar da Najeriya ta yi wajen dakile yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, yana kiran hakan tsayin daka wajen kare dimokuraɗiyya a yammacin Afrika.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Barau ya jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda martanin gaggawa ga bukatar taimakon da Benin ta nema domin dawo da tsarin mulki.
Barau ya jaddada cewa wannan mataki ya nuna jajircewar Najeriya wajen kare tsarin dimokuraɗiyya.
Ya ce: “Mulkin soja ba shi da wurin zama a cikin al’ummarmu. Duk da halin da ake ciki, dimokuraɗiyya ita ce zabin da ya fi dacewa ga yankinmu da nahiyarmu.”
Sanatan ya bayyana cewa saurin martani da ingancin aikin da Najeriya ta yi sun sake tabbatar da matsayin ƙasar a matsayin jagora wajen kare zaman lafiyar dimokuraɗiyya a yammacin Afrika, musamman a wannan lokaci da yankin ke fuskantar tashin-tashina na kin bin tsarin mulki.
Ya haskaka rawar da cibiyoyin ECOWAS, ciki har da majalisar ta ke takawa wajen ƙarfafa haɗin kai, inganta dimokuraɗiyya da kuma haɗa kai kan tsaro domin kauce wa sake faruwar irin waɗannan tashin hankula.
Kiran Barau ga kasashen Afrika
Barau ya kira ƙasashen Yammacin Afrika da su ci gaba da gina ingantattun cibiyoyin dimokuraɗiyya, yana mai jaddada cewa kulawar haɗin gwiwa da hanzarin ɗaukar mataki na da matuƙar muhimmanci wajen kare zaman lafiyar yankin.
Barau ya nanata cewa matakin Najeriya ba wai kawai nuna goyon baya ga ƙasashe maƙwabta ba ne, sako ne cewa dole ne a kare ka’idojin dimokuraɗiyya a kowane hali.
“Daukar mataki cikin gaggawa a kan yunƙurin karɓe mulki ba bisa ƙa’ida ba na aikawa da saƙon cewa dimokuraɗiyya ba abin sassauci ba ce a yammacin Afrika,” in ji shi.
Ya kammala da kira da a ci gaba da haɗin kai tsakanin gwamnatocin yankin da cibiyoyinsu domin tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ita ce ginshiƙin zaman lafiya da tsaro a fadin yammacin Afrika.