Yayin da aka cika shekaru uku da juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya a Jamhuriyar Nijar, makusantan tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, sun sake yin kira da a gaggauta sake shi daga tsarewa.
Masu magana da yawunsa sun bayyana damuwa kan yadda Bazoum da matarsa ke ci gaba da kasancewa a tsare tun bayan juyin mulkin ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ko ba su damar kare kansu ta hanyar shari’a ba.
Sun ce ci gaba da tsare tsohon shugaban ƙasar ba tare da bin ka’idojin doka ba ya saɓa wa ƙa’idodin adalci da haƙƙin ɗan Adam, tare da yin kira ga hukumomin Nijar da su mutunta dokoki da kuma bai wa shari’a damar gudanar da aikinta.
Tun bayan juyin mulkin da ya faru a watan Yulin 2023, gwamnatin sojin Nijar na ci gaba da tsare Mohamed Bazoum a fadarsa da ke Yamai, lamarin da ya janyo martani daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ƙasashen duniya.