Monday, October 19, 2026
HomeTsaroDan majalisar tarayya ya bukaci a’ummar Zamfara su dauki matakin kare kai

Dan majalisar tarayya ya bukaci a’ummar Zamfara su dauki matakin kare kai

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Bungudu da Maru, Abdulmalik Zubairu, wanda aka fi sani da Zannan Bungudu, ya bukaci al’ummar Jihar Zamfara da su ƙara ɗaukar matakan kare rayukansu da dukiyoyinsu sakamakon ci gaba da matsalar rashin tsaro a jihar.

Zannan Bungudu ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar yaɗa labarai ta DCL, inda ya ce akwai buƙatar jama’a su kasance cikin shiri tare da haɗa kai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.

Kalaman nasa sun zo ne bayan sace shugaban Ƙaramar Hukumar Bungudu da wasu ‘yan bindiga suka yi a kwanakin baya, lamarin da ya sake jawo hankalin jama’a kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a wasu sassan jihar.

Sai dai hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya sun bayyana cewa suna ci gaba da gudanar da manyan ayyukan tsaro domin daƙile ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Haka kuma, sun tabbatar da cewa ana ƙarfafa jami’an tsaro tare da faɗaɗa matakan tsaro a yankunan da matsalar ta fi kamari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments