Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAkalla ’yan Najeriya miliyan 16 za su fuskanci barazanar yunwa zuwa Janairun...

Akalla ’yan Najeriya miliyan 16 za su fuskanci barazanar yunwa zuwa Janairun 2027 – Rahoto

Wani sabon rahoto na FEWS NET (Famine Early Warning Systems Network) ya yi hasashen cewa akalla ’yan Najeriya miliyan 16 zuwa miliyan 16.99 za su fuskanci matsananciyar yunwa tare da buƙatar tallafin abinci na gaggawa zuwa watan Janairun 2027.

Rahoton ya bayyana cewa duk da wannan hasashe mai tayar da hankali, an samu ɗan sauƙi idan aka kwatanta da watan Yulin 2026, lokacin da aka kiyasta cewa tsakanin mutane miliyan 20 zuwa 20.99 ne ke cikin irin wannan hali.

A cewar rahoton, ana sa ran girbin amfanin gona na daminar bana zai taimaka wajen rage matsin ƙarancin abinci a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya sa aka rage adadin mutanen da ake hasashen za su fuskanci matsananciyar yunwa.

Sai dai rahoton ya gargaɗi cewa matsalolin tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, sauyin yanayi da kuma ƙarancin damar samun abin yi na ci gaba da barazana ga wadatar abinci, musamman a yankunan da rikice-rikice suka fi kamari.

FEWS NET ya jaddada cewa akwai buƙatar ci gaba da samar da tallafin jin ƙai da kuma aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa samar da abinci da inganta rayuwar al’umma domin rage haɗarin ƙaruwar yunwa a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments