A ranar 26 ga Yulin 1975, shekaru 51 da suka gabata, Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Yammacin Afirka, Sheikh Ibrahim Niass, rasuwa a asibitin St. Thomas da ke birnin Landan na ƙasar Ingila.
Shehin malamin ya rasu yana da shekaru 75 a duniya, bayan ya je Landan a watan Yunin 1975 domin duba lafiyarsa, wanda ya yi daidai da watan Jumada al-Thani na shekarar 1395 bayan Hijira.
Bayan rasuwarsa, an dawo da gawarsa zuwa ƙasarsa ta haihuwa, Senegal, inda aka binne shi a Madina Baye da ke Kaolack, kusa da babban masallacin da ya gina.
Kafin tafiyarsa zuwa Landan, Sheikh Ibrahim Niass ya sanar da iyalansa cewa tafiyar za ta kasance ta ɗan gajeren lokaci, inda ya buƙaci ’ya’yansa da su zauna a gida maimakon su raka shi.
Rasuwar tasa ta girgiza miliyoyin almajiransa da mabiyansa a Yammacin Afirka da sauran sassan duniya. Har zuwa yau, miliyoyin mutane na ci gaba da yi masa addu’ar samun rahama da gafarar Allah, bisa gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen yaɗawa da haɓaka addinin Musulunci.