Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaSanata Rufa’i Hanga ya nemi ra’ayin magoya baya kan makomar siyasarsa

Sanata Rufa’i Hanga ya nemi ra’ayin magoya baya kan makomar siyasarsa

Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rufa’i Sani Hanga, ya umarci kodinetocinsa na ƙananan hukumomi 15 da su koma mazabunsu domin tattaunawa da magoya baya kan makomar siyasarsa, bayan da ya rasa tikitin takarar Sanata a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya.

Rahotanni sun ce Sanatan ya buƙaci kodinetocin su tattara ra’ayoyin magoya baya kan ko ya ci gaba da kasancewa a tafiyar Kwankwasiyya ko kuma ya sauya sheƙa zuwa wata jam’iyyar siyasa da ta nuna sha’awar karɓarsa.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da hasashe kan matakin siyasar da Sanata Hanga zai ɗauka, musamman bayan ganinsa tare da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, a makon da ya gabata.

Haka kuma, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai masa ziyara a gidansa.

Baya ga APC, wank rahoton ya nuna cewa jam’iyyar ADC na daga cikin jam’iyyun da ke ƙoƙarin jawo Sanata Hanga cikinta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments