Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada cewa ginshiƙin zaman aure mai ɗorewa shi ne kyawawan ɗabi’u, haƙuri, yafiya da tausayi, ba tarin dukiya ko kyawun sura kaɗai ba.
Ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ɗaurin aure, inda ya yi kira ga iyalai su ci gaba da tarbiyyar ‘ya’yansu bisa kyawawan dabi’u.
Shettima ya ce aure na daga cikin manyan matakan da ake gwada halayen mutum, domin a cikinsa ne ake nuna gaskiya, haƙuri da jinƙai a rayuwar yau da kullum.
Ya ƙara da cewa iyali mai ƙarfi shi ne tushen al’umma mai ɗorewa, kuma kyawawan dabi’u su ne ke tabbatar da zaman lafiya da ɗorewar aure.