Ƙungiyar kare haƙƙoƙin tattalin arziki da zamantakewa (SERAP) ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman a tilasta wa Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) bayyana cikakkun bayanai kan Naira tiriliyan 211 da aka rubuta a rahoton binciken kuɗin kamfanin na shekarar 2023 a matsayin “Sundry Receivables” da “Accrued Expenses.”
SERAP ta bayyana cewa rahoton ya nuna Naira tiriliyan 107.6 a matsayin kuɗaɗen da ake bin NNPCL, yayin da Naira tiriliyan 103.4 ke matsayin bashin da kamfanin ke bin wasu, ba tare da fayyace waɗanda abin ya shafa ko takardun da suka tabbatar da waɗannan ma’amaloli ba.
Ƙungiyar ta buƙaci kotu ta umarci NNPCL ta bayyana sunayen waɗanda ake bi kuɗin da waɗanda za a biya, tare da duk takardun da aka yi amfani da su wajen shirya rahoton. SERAP ta ce Dokar ’Yancin Samun Bayanai ta ba ’yan Najeriya damar sanin yadda ake tafiyar da dukiyar ƙasa, tana mai cewa har yanzu NNPCL ba ta amsa buƙatar bayanan da ta aika mata ba, kuma ba a sanya ranar fara sauraron ƙarar ba.