Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa a yau Lahadi ne za ta kammala aikin rijistar masu kaɗa ƙuri’a a faɗin Najeriya.
Hukumar ta ce wa’adin da aka sanya tun farko zai ƙare kamar yadda aka tsara, kuma ba za a ƙara masa lokaci ba.
Sanarwar na zuwa ne yayin da dubban ’yan Najeriya ke ci gaba da tururuwa zuwa cibiyoyin rajista domin kammala rijista ko sabunta bayanansu kafin wa’adin ya cika.
INEC ta buƙaci duk masu buƙatar rajista su gaggauta kammala aikin kafin rufe cibiyoyin rajistar.
A kwanakin baya, jam’iyyun adawa da wasu ƙungiyoyin fararen hula sun yi kira ga INEC da ta tsawaita wa’adin rajistar.
Sun bayyana cewa har yanzu akwai mutane da dama da ba su samu damar yin rajista ba saboda cunkoso da kuma wasu matsalolin gudanarwa.
Sai dai INEC ta sake nanata cewa ba ta da shirin tsawaita wa’adin, tana mai cewa an ba da isasshen lokaci domin gudanar da rajistar. Hukumar ta kuma bukaci jama’a su mutunta jadawalin da aka fitar tun da farko.
Hukumar ta ƙara da cewa kammala rajistar masu zaɓe na daga cikin muhimman matakan shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.
Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya su ci gaba da bin dokokin zaɓe tare da shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya ta hanyar yin rajista da kuma amfani da damar kaɗa ƙuri’arsu a ranar zaɓe.