Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jajanta wa al’ummar garin Dangamau da ke ƙaramar hukumar Kusada bayan wata guguwar iska mai ƙarfi tare da ruwan sama ta lalata gidaje, shaguna da kadarori sama da 200.
Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa mutane da dama sun rasa matsugunansu da kuma hanyoyin samun abin dogaro.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Ibrahim Kaula, ya fitar a ranar Lahadi, Radda ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa gwamnati ba za ta yi watsi da su ba.
Ya ce ya umarci hukumomin da abin ya shafa su gaggauta tantance irin barnar da aka yi domin fara kai wa waɗanda abin ya shafa agajin gaggawa.
Gwamnan ya ƙara da cewa an riga an shirya kai kayan agaji da suka haɗa da abinci, matsugunan wucin gadi da sauran kayan buƙata ga mutanen da suka rasa gidajensu.
Haka kuma, ya buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an agajin gaggawa haɗin kai yayin da gwamnati ke ƙoƙarin dawo da al’amura yadda suke.