Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Bungudu, Hon. Nura NU. a Zamfara a wasu hare-hare da suka kai cikin dare.
Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin gidan shugaban inda suka yi awon gaba da shi tare da wasu daga cikin iyalansa.
A harin da aka kai Bungudu, an ruwaito cewa jami’in tsaron shugaban ƙaramar hukumar ya rasa ransa bayan da maharan suka harbe shi, yayin da ɗan uwan shugaban ƙaramar hukumar ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan hare-haren ba.