Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKotu a Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa bayan kashe...

Kotu a Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa bayan kashe wata mata mai ciki

Wata Babbar Kotu da ke Jihar Kano ta yanke wa Shuaibu Abdulkadir hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe wata mata mai suna Rumaisa Shuaibu, mai shekaru 22, wacce ke ɗauke da ciki a lokacin da lamarin ya faru.

Mai shari’a Farida Dan Baffa ta bayyana a hukuncin da ta yanke ranar Juma’a cewa masu gabatar da ƙara sun gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da cewa wanda ake tuhuma ne ya aikata laifin.

An fara gurfanar da Shuaibu Abdulkadir a gaban kotu tun a watan Agustan 2025, inda aka fara sauraron shari’ar kafin kotun ta yanke hukuncin kisa a kansa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments