Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro’Yan Bindiga sun hallaka manoma 24 a Zamfara – Amnesty International

’Yan Bindiga sun hallaka manoma 24 a Zamfara – Amnesty International

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ce ’yan bindiga sun kashe manoma 24 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai yankin Sauna Ruwan Gora da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

A cewar ƙungiyar, maharan sun buɗe wa manoman da ke aiki a gonakinsu wuta, yayin da wasu suka tsere da raunuka masu tsanani.

Ta kuma bayyana cewa har yanzu akwai wasu manoman da ba a san inda suke ba bayan harin.

Amnesty International ta ce hare-haren da ake ci gaba da samu na nuna buƙatar ƙara inganta tsaro, tare da kira ga hukumomi su kare rayukan al’umma da kuma gurfanar da waɗanda ke da hannu a irin waɗannan hare-hare a gaban kotu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments