Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaAPC ta mayar wa Kwankwaso martani kan kalamansa game da matsalar tsaro

APC ta mayar wa Kwankwaso martani kan kalamansa game da matsalar tsaro

Jam’iyyar APC ta yi watsi da sukar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalolin tsaro da tattalin arziki, tana mai cewa kalaman nasa na da alaƙa da neman goyon bayan siyasa gabanin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce wasu na ƙoƙarin hana sauye-sauyen gwamnati nasara ne saboda suna cin moriyar tsohon tsarin da ake son gyarawa.

Sai dai ƙungiyar Kwankwasiyya ta dage cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika babban nauyin da ke kanta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kakakin ƙungiyar, Dakta Habibu Saleh Mai Lemo, ya ce kowane ɗan Najeriya na iya tabbatar da irin ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a sassan ƙasar.

A wani ɓangare kuma, tsohon shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya soki shirin Kwankwaso na tattaunawa da ’yan bindiga, yana mai cewa hakan na iya ƙarfafa masu aikata laifuka maimakon kawo ƙarshen matsalar tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments