Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi gargaɗi ga al’umma kan wasu da ake zargin suna damfarar masu son shiga shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shiryawa.
Hukumar ta bayyana cewa wasu na karɓar kuɗi daga jama’a da sunan za su taimaka musu wajen yin rajista ko tabbatar da sun shiga cikin shirin, lamarin da ta ce ba shi da sahihanci.
Hisbah ta jaddada cewa ba a amince wani mutum ko ƙungiya su karɓi kuɗi daga masu neman shiga shirin ba, tare da kira ga jama’a da su guji bai wa kowa kuɗi da wannan dalili.
Hukumar ta kuma buƙaci duk wanda ya ci karo da irin waɗannan masu damfara da ya gaggauta kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa domin ɗaukar matakin da ya dace.