Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya kai wa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NDC, Sanata Kabiru Gaya, ziyara a gidansa da ke Yaounde Street, Abuja, a daren Litinin.
Majiyoyi sun ce ganawar ta ɗauki kusan mintuna 45, inda aka tattauna muhimman batutuwan siyasa gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa an cimma matsaya kan yiwuwar Sanata Kabiru Gaya komawa jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga Sanata Kabiru Gaya ko jam’iyyar APC da ta tabbatar da wannan iƙirari.