Saturday, October 17, 2026
HomeWasanniFIFA ta raba makudan kudade bayan kammala Gasar Kofin Duniya ta 2026

FIFA ta raba makudan kudade bayan kammala Gasar Kofin Duniya ta 2026

Hukumar FIFA ta raba kuɗaɗe mafi yawa a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya bayan kammala gasar 2026, inda ƙasashe 48 da suka halarta suka raba jimillar Dala miliyan 871.

Zakaran gasar, Sifaniya, ta samu Dala miliyan 51 (kimanin naira biliyan 70.36), bayan ta doke Argentina a wasan ƙarshe da ci 1-0.

Ita kuwa Argentina ta tashi da Dala miliyan 33 saboda zama ta biyu.

FIFA ta bayyana cewa gasar bana ita ce ta fi kowacce girma da kuma samar da kuɗaɗen shiga tun bayan fara Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 1930.

Adadin kuɗin da kowace ƙasa ta samu ya danganta ne da irin matakin da ta kai a gasar, yayin da nasarar Sifaniya ta sanya ta zama ƙasar da ta fi kowa samun kuɗin a wannan karo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments