Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a kauyen Kururawa da ke yankin Lakwaya, karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano.
‘Yan bindiga na ci gaba da yin kutse daga Katsina zuwa wasu kauyukan jihar Kano, inda suke addabar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Mazauna yankin sun nuna damuwa kan hare-haren ‘yan bindiga, inda suka yi kira ga gwamnatin Kano kan ta kawo musu daukin gaggawa