Gwamnatin Amurka ta gargaɗi ’yan ƙasarta da su guji yin balaguro zuwa wasu ƙasashen Afirka guda 23, tana mai bayyana matsalolin tsaro a matsayin babban dalilin ɗaukar wannan mataki.
A cewar gwamnatin Amurka, ƙasashen da abin ya shafa na fuskantar ƙalubalen tsaro da suka haɗa da hare-haren ta’addanci, satar mutane, rikice-rikicen cikin gida da sauran matsalolin da ka iya jefa baƙi cikin haɗari.
Daga cikin ƙasashen da ta bayyana akwai Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso, waɗanda suka daɗe suna fama da matsalolin tsaro a wasu yankunansu.
Amurka ta kuma bayyana cewa a wasu daga cikin waɗannan ƙasashe, ƙarfinta na kai agajin gaggawa ko taimakon ofishin jakadancinta ga ’yan ƙasarta na da matuƙar iyaka saboda halin da ake ciki.
Gwamnatin ta shawarci ’yan ƙasarta da su ci gaba da bibiyar sabbin bayanan tsaro tare da kauce wa balaguro zuwa yankunan da aka ayyana a matsayin masu haɗari har sai an samu sauyin yanayi.