Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSanya wa cibiyoyi da hanyoyi sunan Tinubu ya jawo cece-ku-ce a Najeriya

Sanya wa cibiyoyi da hanyoyi sunan Tinubu ya jawo cece-ku-ce a Najeriya

Matakin gwamnatin tarayya na sanya sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga wasu manyan cibiyoyi da hanyoyin gwamnati ya ci gaba da haifar da suka daga sassa daban-daban na ƙasar.

Sabon matakin da ya fi jan hankali shi ne sanya wa babbar hanyar Lagos–Calabar Coastal Highway sunan Shugaba Tinubu, wanda gwamnatin ta ce an yi ne domin karrama gudunmawarsa da hangen nesansa wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.

Sai dai masu sukar matakin sun bayyana cewa bai dace a riƙa sanya sunayen shugabanni masu ci kan kadarorin gwamnati ba.

A cewarsu, hakan na iya nuna tamkar ana mayar da kadarorin al’umma mallakin mutum ɗaya, tare da ƙarfafa al’adar yabon shugabanni fiye da kima.

Wasu kuma na ganin irin waɗannan sunaye ya kamata a riƙa ba su ne bayan shugabanni sun kammala wa’adinsu ko kuma bisa cikakken matsaya da amincewar al’umma.

A gefe guda, masu goyon bayan matakin suna cewa babu laifi a karrama shugaba idan ya kawo gagarumin ci gaba da ayyukan raya ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments