Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su tare da dakile hare-haren da ake zargin ‘yan ta’adda sun shirya kai wa a ƙananan hukumomin Anka da Kaura Namoda na Jihar Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya ce an samu nasarar ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka bai wa sojoji damar cafke shirin ‘yan ta’addan kafin su kai harinsu.
A farmakin farko da aka kai a yankin Tungan Kudaduku da ke ƙaramar hukumar Anka, sojoji sun fafata da ‘yan ta’addan a musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji tare da barin sansaninsu. Bayan bincike, an gano tare da ceto fararen hula biyar da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba.
A wani samame daban da aka kai a Ungwan Rogo da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda, sojoji sun sake fafatawa da ‘yan ta’addan, inda suka tilasta musu guduwa tare da ceto ƙarin mutane takwas da aka yi garkuwa da su. Haka kuma an ƙwato motoci biyu da ake zargin ‘yan ta’addan sun bari yayin da suke tserewa.
Rundunar ta ce an miƙa dukkan mutanen 13 da aka ceto ga hukumomin da abin ya shafa domin ba su kulawar lafiya, tantance su da kuma haɗa su da iyalansu. Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da kai farmaki domin hana ‘yan ta’adda samun mafaka da tabbatar da zaman lafiya a Zamfara da sauran jihohin yankin Arewa maso Yamma.