Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyarar ban girma ga Sanata Rufa’i Sani Hanga, wanda shi ne kaɗai sanatan jam’iyyar NDC daga Jihar Kano, a gidansa da ke Abuja a daren Laraba.
Mai taimaka wa Sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Umar Saminu Mai-Adashi, ya ce ganawar ta gudana cikin mutunci da fahimtar juna, inda bangarorin biyu suka tattauna kan muhimman batutuwan siyasar Najeriya da hanyoyin ƙarfafa dimokuraɗiyya da ci gaban ƙasa.
Ziyarar ta ƙara ruruta jita-jitar cewa Sanata Hanga na iya sauya sheƙa zuwa APC, musamman bayan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka ce an nuna masa wariya a cikin jam’iyyarsa ta NDC.
Hanga, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya kuma aminin Rabiu Musa Kwankwaso, ya koka cewa an cire shi daga jerin ‘yan takarar da aka cimma matsaya a kansu, lamarin da ya hana shi samun tikitin takarar sanata.
Rahotanni sun ce shugabannin APC na ci gaba da ƙoƙarin jawo Hanga zuwa jam’iyyarsu, musamman bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma APC. Sai dai har zuwa yanzu Sanata Hanga bai bayyana a hukumance cewa zai sauya sheƙa ba, duk da cewa ana kallon ganawarsa da shugaban APC a matsayin wata alama ta yiwuwar hakan.