Wani limamin cocin Katolika ɗan asalin Najeriya, Reverend Benjamin Okwy Madu, ya rasu bayan ya kashe kansa a gidansa da ke Lynnfield, jihar Massachusetts ta Amurka, kwanaki kaɗan bayan an umarce shi da ya koma Najeriya sakamakon ƙarewar bizar zamansa.
Rahotanni sun ce Madu ya mutu ne a ranar 2 ga Yuli, 2026, yayin da bizar aikinsa za ta ƙare a ranar 29 ga Yuli, 2026. Tun daga shekarar 2021 yake aiki a ƙarƙashin Archdiocese na Boston a matsayin limamin asibiti da kuma limamin coci a yankin Cape Ann.
An bayyana cewa marigayin ya riƙa nuna damuwa tare da bayyana wa na kusa da shi cewa yana fargabar abin da zai same shi idan aka tilasta masa komawa Najeriya. Wannan fargaba ce ake zargin ta ƙara tsananta masa kafin mutuwarsa.
Hukumomin cocin Archdiocese na Boston sun tabbatar da rasuwarsa tare da bayyana alhininsu, suna yabawa gudunmawar da ya bayar wajen hidimarsa ga coci da al’umma a lokacin da yake aiki a Amurka.
Lamarin ya tayar da muhawara kan muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da tallafa wa ma’aikatan addini da sauran mutane da ke fuskantar matsin lamba ko damuwa sakamakon matsalolin rayuwa da na ƙaura.