Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kebbi za ta ɗaura auren gata ga mutane 300

Gwamnatin Kebbi za ta ɗaura auren gata ga mutane 300

Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da auren gata ga mutum 300 da suka haɗa da Musulmi da Kiristoci daga sassa daban-daban na jihar.

An tsara gudanar da bikin ɗaurin auren ne a ranar 27 ga Yulin 2026.

Shirin zai gudana ne haɗin gwiwa da gidauniyar (NANAS), inda aka zaɓi wadanda za a aurar daga ƙananan hukumomi 21 na jihar.

An bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne bisa ƙa’idojin da aka shimfiɗa domin tabbatar da adalci da cancanta.

Shugaban kwamitin shirya shirin, Alhaji Suleiman Argungu, ya ce waɗanda aka zaɓa sun haɗa da marayu, zawarawa da waɗanda aka raba aurensu, bayan sun cika dukkan sharuɗɗan addini da na doka da ake buƙata kafin ɗaura aure.

Ya ƙara da cewa wannan shi ne karo na uku da gwamnatin jihar ke gudanar da irin wannan shiri, bayan nasarorin da aka samu a shekarun 2024 da 2025.

Haka kuma, Gwamna Nasir Idris ya amince da biyan sadaki na N250,000 ga kowace amarya cikin amaren 300 da za su ci gajiyar shirin.

Baya ga biyan sadaki, gwamnati tare da abokan haɗin gwiwarta za su samar wa sabbin ma’auratan kayan ɗaki, kayan abinci da sauran kayan amfanin gida domin tallafa musu wajen fara rayuwar aure.

Haka kuma, an tabbatar da cewa dukkan ma’auratan sun yi gwaje-gwajen lafiya da suka haɗa da na genotype, HIV/AIDS, ciki da sauran gwaje-gwajen da doka ta tanada kafin ɗaura aure.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments