Hedikwatar Tsaron Najeriya ta musanta ikirarin da wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya yi cewa sojojin Amurka ne suka kwace dimbin na’urorin leken asiri da bayanan sirri daga sansanonin ‘yan ta’adda da ke Najeriya.
A cewar Hukumar Tsaron, bayanan da aka yaɗa ba su yi daidai da abin da ya faru ba, domin ba sojojin Amurka ne suka kwace kayayyakin ba kamar yadda aka bayyana.
Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ce ta miƙa waɗannan na’urori da bayanan sirri ga Amurka a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwar da ƙasashen biyu ke yi wajen musayar bayanan sirri da yaƙi da ta’addanci.
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya samo asali ne daga kyakkyawar alaƙar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, wanda ke da manufar ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro.
Hedikwatar Tsaron ta jaddada cewa ya dace a riƙa bayyana irin waɗannan bayanai yadda suka faru, domin kauce wa yaɗa bayanan da ka iya haifar da ruɗani game da rawar da Najeriya ke takawa a yaƙi da ta’addanci.