Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta kama motoci 81 da suka karya dokokin hanya, ciki har da motocin da ke yawo ba tare da lambar rajista ba da kuma waɗanda suka rufe lambobinsu ba bisa ƙa’ida ba.
Ibrahim Adamu Bakori, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce rundunar za ta ci gaba da aiwatar da dokoki domin tabbatar da tsaro da bin ƙa’idojin zirga-zirga a faɗin jihar.
Ya kuma buƙaci al’umma da su kai rahoton duk wani jami’in ɗan sanda da suka gani yana karya doka ta hanyar kiran lambobin 09134558533 ko 080115657624, domin rundunar ta ɗauki matakin da ya dace.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da al’umma wajen inganta tsaro, tabbatar da bin doka da oda, da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Kano.