Akalla manoma tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka fada hannun ’yan bindiga bayan wani hari da aka kai a wani ƙauye da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun afka wa ƙauyen ne tare da buɗe wuta kan mazauna yankin, kafin daga bisani su yi garkuwa da mutane da dama.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa harin ya zo ne a daidai lokacin da aka fara daminar bana, lokacin da manoma ke komawa gonakinsu domin gudanar da ayyukan noma.
Rahotannin sun kuma nuna cewa ’yan bindigar na kai hare-hare kan manoma, musamman waɗanda ake zargin sun ƙi ko suka kasa biyan kuɗaɗen harajin da suke kakabawa mazauna yankunan karkara.
Lamarin ya sake tayar da hankalin mazauna yankin, yayin da ake kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma tabbatar da tsaron manoma a lokacin noman damina.