Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAPC ta ce za ta lallashi ’yan takarar da aka sauya sunansu

APC ta ce za ta lallashi ’yan takarar da aka sauya sunansu

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa za ta lallashi ’yan takarar da aka sauya sunayensu bayan kammala tantance masu neman takara a matakai daban-daban.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa za ta lallashi ’yan takarar da aka sauya sunayensu bayan kammala tantance masu neman takara a matakai daban-daban.

Jam’iyyar ta ce ta tantance kimanin ’yan takara 2,500 da suka nemi tikitin takara a ƙarƙashin inuwarta, inda ta maye gurbin wasu daga cikinsu da waɗanda ta fi muradi.

Tuni APC ta fara miƙa sunayen ’yan takarar da aka amince da su ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC, domin ci gaba da shirye-shiryen zaɓe.

Daraktan Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Bala Ibrahim, ya ce an bai wa waɗanda aka zaɓa takardun shaidar takara, sannan aka miƙa sunayensu ga INEC domin wallafawa.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta yi ƙoƙarin sasanta da lallashin waɗanda aka sauya sunayensu domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a cikin APC.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments