Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAtiku ya ba Tinubu wa’adin mako guda ya binciki zargin badakalar hukumar...

Atiku ya ba Tinubu wa’adin mako guda ya binciki zargin badakalar hukumar bogi

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin kafa wata hukuma ko ta bogi a cikin gwamnatin tarayya.

Atiku ya ce lamarin ya wuce zarge-zargen ƙirƙirar takardu na bogi kawai, yana mai cewa ya haifar da tambayoyi masu yawa kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.

Ya ba Shugaba Tinubu wa’adin mako guda da ya ƙaddamar da sahihin bincike tare da bayyana sakamakon binciken ga jama’a domin tabbatar da gaskiya da ɗaukar matakan da suka dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments