Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKotu ta tabbatar da David Mark a matsayin shugaban ADC

Kotu ta tabbatar da David Mark a matsayin shugaban ADC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ADC, bayan ta yi watsi da ƙarar da ɗan majalisar wakilai, Leke Abejide, ya shigar yana ƙalubalantar sabon shugabancin jam’iyyar.

Mai shari’a Musa Liman ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar, saboda ta shafi harkokin cikin gida na jam’iyya.

Ya kuma bayyana cewa mai ƙarar bai bi hanyoyin sasanci da kundin tsarin jam’iyyar ya tanada ba kafin ya garzaya kotu.

Kotun ta kuma tabbatar da cewa naɗin David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugabannin ADC ya yi daidai da kundin tsarin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.

Bayan yanke hukuncin, Atiku Abubakar, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da fafutukar neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments