Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta kama wasu mutane uku da ake zargi da lalatawa tare da satar wayoyin lantarkin da ke haɗe da na’urar wutar lantarki (transformer) a garin Dapchi, Ƙaramar Hukumar Bursari.
Mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan samun rahoton lalata layukan wutar lantarki. Ya bayyana sunayensu da Danladi Saleh mai shekaru 30, Usman Ibrahim mai shekaru 33, dukkansu mazauna Dapchi, da kuma Mohammed Ali mai shekaru 23 daga Ƙaramar Hukumar Geidam.
Rundunar ta ce jami’anta sun kama waɗanda ake zargin da misalin ƙarfe 6 na safe, inda aka same su da tarin wayoyin lantarki da aka yanke ana zargin sun shirya sayar da su.
Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun cire wayoyin lantarkin, lamarin da ya haddasa rushewar wasu sandunan wuta a yankin. Rundunar ta ce bincike na ci gaba domin kamo sauran waɗanda ake zargi da hannu a lamarin tare da ƙwato ƙarin kayayyakin da aka sace.