Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya tabbatar da cewa daya daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta amince da su a Hukumar Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC) shi ne sauya kakin da masu yi wa ƙasa hidima ke sanyawa.
Ministan ya bayyana cewa daga yanzu gwamnatin tarayya za ta maye gurbin kakin NYSC da tufafin Adire (Kamfala) da ake kerawa a cikin Najeriya.
Olawande ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin The Morning Brief na tashar Channels TV a ranar Alhamis.
Ya ce manufar wannan sauyi ita ce bunƙasa masana’antun cikin gida, ƙarfafa harkar sarrafa yadi a Najeriya, da kuma tabbatar da cewa kuɗin gwamnati na ci gaba da zagayawa a cikin tattalin arzikin ƙasar.
A cewarsa, ana samar da kayan Adire a jihohin Ogun da Kwara tare da sauran masana’antun yadi da ke faɗin ƙasar, don haka ya dace gwamnati ta rika amfani da kayayyakin da ake kerawa a gida.