Dan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce bai kamata kotu ta zama dandalin gudanar da yaƙin siyasa ba, yana mai cewa kotuna na daga cikin muhimman ginshiƙan tabbatar da dimokuraɗiyya.
Atiku ya bayyana hakan ne bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta tabbatar da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ADC.
A cewarsa, ya kamata a mutunta hukuncin kotuna tare da guje wa amfani da su wajen fafatawar siyasa.