Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiCi gaba da karɓo bashi zai ƙara jawo wa Najeriya koma bayan...

Ci gaba da karɓo bashi zai ƙara jawo wa Najeriya koma bayan tattalin arziƙi – Masana

Dr. Abdulnasir Turawa Yola: Sabbin basussukan da gwamnatin Tinubu ke karɓa ba su da amfani ga tattalin arziƙin Najeriya.

Masanin tattalin arziƙi, Dr. Abdulnasir Turawa Yola, ya bayyana cewa ci gaba da karɓo bashin da Najeriya ke yi ba zai amfani ƙasar ba, sai dai ya ƙara jefa tattalin arziƙinta koma baya.

A tattaunawarsa da Iconic Times, Dr. Abdulnasir ya ce matsalar ba wai karɓo bashi kaɗai ba ce, har ma da yadda ba a amfani da kuɗaɗen bashin wajen aiwatar da ayyukan da suka dace.

Ya ƙara da cewa: “bai kamata gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake karɓar wani sabon bashi ba”.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan Bankin Duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen Dala biliyan 1.25 domin tallafa wa shirye-shiryen bunƙasa zuba jari, ƙarfafa harkokin kasuwanci da kuma inganta tattalin arziƙin ƙasar.

Bankin ya ce sabon bashin wani ɓangare ne na tsarin haɗin gwiwa da Najeriya na shekarun 2026 zuwa 2032, wanda zai mayar da hankali kan sauye-sauyen tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, bunƙasa jarin masu zaman kansu da kuma inganta rayuwar al’umma.

Sai dai Dr. Abdulnasir Turawa ya yi gargadin cewa “idan ba a tabbatar da amfani da irin waɗannan basussuka yadda ya kamata ba, za su ƙara nauyin tattalin arziƙin ƙasar maimakon kawo ci gaba“.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments