Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMutane 4 sun rasu bayan fashewar wata na'ura a Borno

Mutane 4 sun rasu bayan fashewar wata na’ura a Borno

Fashewar wata na’ura ya yi sanadiyyar mutuwar mutun hudu

Wasu matasa huɗu sun rasa rayukansu bayan fashewar wata na’urar IED a bayan tashar mota da ke unguwar Wajari,a karamar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Jami’in hulɗa da Jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya bayyana cewa na’urar ta fashe ne da misalin ƙarfe 12:40 na rana.

Rundunar ‘yan sanda ta ce matasan sun samo na’urar ne a daji, suka kawo ta wani tantin wucin-gadi a bayan tashar mota, inda ta fashe a lokacin da suke taɓa ta.

Wani yaro mai shekaru 12, Mustapha Tijja, wanda ya kasance a wurin a lokacin fashewar, ya samu munanan raunuka, yayin da aka kai shi asibitin FHI 360 da ke Banki domin samun kulawa.

Waɗanda suka mutu sun hada da Awana Mustapha, mai shekaru 15, Malum Modu, 14, Lawan Ibrahim 12 da Modu Abacha, 12.

Kwamishinan ‘yan sanda, Naziru Abdulmajid, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya shafa, tare da yin kira ga jama’a, musamman yara, da su guji taɓa kowanne abu da ba a sani ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments