Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta ce ta yi nasarar lalata sansanin ‘yan bindiga da kama bakwai daga cikinsu da makamansu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito rundunar na cewa ta gudanar da samamen ne tare da hadin gwiwar ƙungiyar mafarauta.
Nasarar ta fara ne da kama wani mai suna Abdullahi Ibrahim a ƙauyen Tilde ranar 23 ga watan Nuwamba, inda ya bayyana sunayen abokan hulɗarsa da ke garkuwa da mutane a Gombe da Bauchi da Adamawa.
Sai dai dakarun ‘yan sanda da na mafarauta sun kai ga kama mutum shida bayan wata fafatawa da ‘yan bindigan, inda suka ƙwace makaman su.
Rundunar ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun bayyana cewa sun samu kuɗaɗe ta hanyar satar mutane da suka kai kusan naira miliyan 150.