Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeDukkanin abin da India ke bukata na makamashi, za mu bata –...

Dukkanin abin da India ke bukata na makamashi, za mu bata – Putin

Shugaba Putin ya ce Rasha a shirye take ta samar wa India man fetur, a yayin da kasar ke fuskantar matsin lamba kan ta daina sayen man Rasha.

Mista Putin wanda a yanzu haka ke ziyara an India, ya shaida wa Firaminista Narendra Modi cewa kasarsa ta kasance abar dogaro wajen samar wa Indiya duk abin da take nema a fannin makamashi.

Amurka na zargin Indiya da tallafawa yakin Rasha an Ukraine da kudi ta hanyar siyan man Rasha, kuma ta sake kakaba wa kayyayakin India da ake shigarwa kasar takunkumi.

Ziyarar tasa dai na aika wani muhimmin sako daga indiya cewa ba za ta bari matsin lambar Amurka na sanya mata haraji ya yi tasiri a kanta ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments