Akalla mutane 19 sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai kauyen Kawel da ke gundumar Mushere, karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin karfe 11:40 na dare a ranar Lahadi, lokacin da maharan suka mamaye kauyen tare da bude wuta kan mazauna yankin, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin, Malo Bitrus, ya ce maharan sun afkawa gidaje tare da harbe-harbe ba kakkautawa, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane 19 da jikkatar wasu da dama.
Shugaban matasa na karamar hukumar Bokkos, Christopher Luka, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa sun sanar da jami’an tsaro cikin gaggawa domin kai dauki.
Lamarin ya sake jefa al’ummar yankin cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakan dakile hare-haren da ke yawaita a jihar Filato.