Mutum takwas sun rasa rayukansu a wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Gulma, da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 3:00 na rana a ranar Litinin, bayan wani makiyayi mai suna Yaron Buba Dogo ya bari shanunsa suka shiga gonar Alhaji Aminu Ala, inda suka lalata amfanin gona.
An ce rikici ya ɓarke tsakanin su, inda makiyayin ya caka wa manomin wuƙa a wuya har ya mutu.
Bayan faruwar lamarin, wasu fusatattun mutane sun taru suka kashe makiyayin tare da ƙona gawarsa. Daga baya kuma aka kai hare-hare kan wasu mazauna al’ummar da abin ya shafa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na dakile rikicin, an kashe ƙarin mutum huɗu tare da ƙona gawarsu har ba a iya gane su ba.
Ya ƙara da cewa daga baya an sake gano gawar wasu mutum biyu a wata gona da ke wajen garin Gulma. Haka kuma, ’yan sanda sun ceto mutum biyar, ciki har da wata mata, tare da kai su ofishin ’yan sanda na Argungu domin kare lafiyarsu.
Rundunar ta ce an tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa zuwa yankin, yayin da gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita domin dawo da zaman lafiya da hana rikicin ƙara kamari.
Wata majiya ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga wata tsohuwar gaba tsakanin manomin da makiyayin, bayan da a baya shanun makiyayin suka shiga gonar manomin, wanda ya yi sanadin karya ƙafar ɗaya daga cikin shanun. Ana zargin wannan ne ya haifar da sabon rikicin da ya ƙare da asarar rayuka.