Mutum shida sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka maƙale a kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan, bayan wani mummunan hatsarin da ya rutsa da motoci da dama.
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne a daren Juma’a a yankin kofar karɓar kuɗin hanya ta Ibadan, inda tankokin gas, manyan motoci da ƙananan motoci suka yi taho-mu-gama, lamarin da ya haddasa gobara.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo ta bayyana cewa an ceto mutum takwas daga cikin tarkacen motocin, sannan aka miƙa su ga Hukumar FRSC domin samun kulawar likitoci. Binciken farko ya nuna cewa matsalar birki ce ta haddasa hatsarin.
Lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa na sa’o’i masu yawa, inda daruruwan matafiya suka maƙale a hanya. Hukumar kashe gobara ta shawarci direbobi da su tabbatar motocinsu na cikin ƙoshin lafiya tare da tanadar na’urar kashe gobara domin rage haɗarin irin waɗannan abubuwa.