Fusatattun matasan sun banka wa ofishin ’yan sanda na Isan da ke Ƙaramar Hukumar Oye a Jihar Ekiti wuta, bayan zargin cewa jami’an ’yan sanda sun harbe wani matashi.
Rahotanni sun ce matasan sun fara zanga-zangar ne bayan wani bidiyo da ya nuna wani matashi kwance cikin jini ya yaɗu a kafafen sada zumunta. An ce matashin ya je filin wasa ne domin kallon wasan ƙwallo lokacin da lamarin ya faru.
A cewar wani jami’in ’yan sanda da ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun kai hari kan ofishin da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, inda suka ƙone ginin tare da lalata motoci da wasu kayayyaki.
Jami’in ya ce ɗaya daga cikin ’yan sandan da suka jikkata na cikin mawuyacin hali a asibiti. Ya kuma bayyana cewa jami’an rundunar Mobile Police sun isa wurin cikin gaggawa, lamarin da ya hana maharan mamaye garin.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta lalata ginin ofishin, motoci biyar, janareta da sauran kayayyaki. Sai dai daga baya jami’an tsaro sun samu nasarar dawo da zaman lafiya a yankin.
Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.