An yi jana’izar Isma’il Makaye, matashin da ke sana’ar sayar da kayan kwalliya a unguwar Hotoro, bayan rasuwarsa a wani gida da ake zargin na budurwarsa ce.
Wani makusancinsa ya ce a same shi cikin mummunan hali bayan wata mata ta nemi agaji da safiyar Juma’a.
Daga nan aka garzaya da shi zuwa Asibitin Nassarawa, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Rahotanni sun ce ’yan sanda sun tsare matar domin gudanar da bincike kan abin da ya faru, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai.
An yi jana’izar marigayin a unguwar Unguwa Uku ’Yan Awaki da ke Kano.