Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta fara kirga ƙuri’u a zaɓen cike gurbi na mazabar Tarayya ta Dawakin Kudu/Warawa da ke Jihar Kano, bayan kammala kaɗa ƙuri’a.
An gudanar da zaɓen ne domin cike gurbin da marigayi ɗan majalisa Muhammad Danjuma Hassan ya bari bayan rasuwarsa a watan Afrilu. Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana ba tare da samun tashin hankali ko wani hargitsi ba.
Sai dai an lura da ƙarancin fitowar masu zaɓe a rumfunan zaɓe, lamarin da ya tayar da damuwa kan rashin sha’awar jefa ƙuri’a.
’Yan takara uku ne suka fafata a zaɓen, waɗanda suka haɗa da Rabiu Shuaibu na APC, Lawan Garba Haruna na APM da Abubakar Yahaya Muhammad na LP.
Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce rashin halartar manyan jam’iyyun adawa irin su PDP, ADC da NDC na iya bai wa jam’iyyar APC damar samun gagarumar fa’ida a zaɓen.