Dakarun Rundunar Sojin Najeriya da ke gudanar da Operation CLEAN SWEEP sun kuɓutar da wani mutum mai suna Nura Yar’adua da aka yi garkuwa da shi, tare da rusa maboyar ‘yan ta’adda da dama a Jihar Katsina.
A cewar majiyoyin soji, dakarun 17 Brigade Strike Group, tare da tawagar kai ɗaukin gaggawa da jami’an runduna ta 8, sun gudanar da farmakin ne domin tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda, katse hanyoyin samun kayan aiki da kuma ƙarfafa tsaro a yankin Arewa maso Yamma.
Rahotanni sun ce a rana ta huɗu na aikin, dakarun sun kai samame a yankunan Tuga da kewaye a Ƙaramar Hukumar Matazu, bayan samun sahihan bayanan sirri da goyon bayan hare-haren sama na Operation FANSAN YAMMA.
Haka kuma, sojojin sun kutsa cikin dajin Fafu, wanda ake zargin ya kasance ɗaya daga cikin manyan mafakar ‘yan ta’adda, a wani mataki na ci gaba da murƙushe ayyukan masu aikata laifuka.