Tsohon gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu (Talban Minna), ya kare martabar marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, inda ya bayyana cewa masu yi masa suka ba su da cikakken ilimin tarihinsa da gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Arewa.
Yayin wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai a Abuja, Mu’azu Aliyu ya ce Sardauna jagora ne mai hangen nesa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bunƙasa ilimi, ƙarfafa haɗin kai da kuma ciyar da Arewacin Najeriya gaba.
Ya ce zarge-zargen da ake yi wa Sir Ahmadu Bello ba kawai suna nuna rashin fahimtar tarihi ba ne, har ila yau suna nuna rashin girmama irin muhimmiyar rawar da ya taka wajen shimfiɗa tubalan ci gaban Arewa da Najeriya gaba ɗaya.
Talban Minna ya kuma shawarci matasa da su riƙa neman ingantattun bayanan tarihi tare da nazarin ayyuka da gudunmawar shugabannin da suka gabata kafin su yanke hukunci a kansu. A cewarsa, tarihin Sardaunan Sakkwato ya kamata a kiyaye shi tare da ba shi mutuncin da ya dace.