Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAPC ta yi fatali da kiran Tinubu ya yi murabus saboda matsalar...

APC ta yi fatali da kiran Tinubu ya yi murabus saboda matsalar tsaro

APC ta kare Tinubu, ta ce yana kokarin magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.

Jam’iyyar APC ta yi watsi da bukatar wasu jam’iyyun adawa da suka hada da ADC, PDP, SDP, NDC da sauran su na neman Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus saboda matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.

Bukatar ta biyo bayan sukar da marasa rinjaye a Majalisar Wakilai suka yi kan yadda gwamnati ke tafiyar da al’amuran tsaro da tattalin arziki.

Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Fred Agbedi, ya ce Najeriya na fuskantar mawuyacin hali, inda ya bukaci Shugaba Tinubu ya dakatar da shirye-shiryen siyasar 2027 tare da ayyana shirin gaggawa na watanni shida domin magance matsalolin tsaro da farfaɗo da tattalin arziki.

Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa da ya nuna ingantaccen jagoranci ko kuma ya sauka daga mulki idan ba zai iya shawo kan matsalolin ba.

Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi fatali da wannan kira, yana mai cewa siyasa ce ta haddasa irin waɗannan kalamai.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu na ci gaba da ɗaukar matakan inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziki, yana mai jaddada cewa ƙalubalen tsaro da tattalin arziki ba Najeriya kaɗai ke fuskanta ba, domin har da manyan ƙasashe kamar Amurka da Birtaniya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments