Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiPeter Obi: Zan yi sulhu da yan ta’addan dake son ajiye makamai...

Peter Obi: Zan yi sulhu da yan ta’addan dake son ajiye makamai idan na ci zaben a 2027

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta rungumi hanyar sulhu da masu aikata laifuka da suka nuna aniyar daina tashin hankali da miƙa makamansu idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.

Obi ya ce za a ba waɗanda suka tuba tare da amincewa da zaman lafiya damar sake shiga cikin al’umma, yayin da hukumomin tsaro za su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace kan waɗanda suka ƙi daina aikata ta’addanci da sauran munanan laifuka.

Ya jaddada cewa manufarsa ita ce dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar tare da rage yawan rikice-rikicen da suka addabi al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments